Kyautar kudin da aka ba izala abuhu ya janyo cecekuce


A jiya Asabar ne aka kawo karshen wa'azin jiha da 'Kungiyar Izalatul Bidi'ah wa Ikamatus Sunnah ta shirya a jihar Zamfara. Taron wanda ya hada manyan Malaman Kungiyan da suka hada shugabanta na Kasa Shaik Abdullahi Bala Balau, Babban Sakataren ta Shaik Kabiru Haruna Gombe, Malam Abubakar Giro da sauran manyan Malamai ne suka gudanar da wa'azi a wajen.


Babban abinda ya jawo cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta na 'Facebook' shine yadda aka bayyana tare da nuna buhun kudi da gwamnan jihar Abdul-Aziz Yari ya bayar ga 'Kungiyar wanda wasu majiyoyi suna cewa kudin ya kai naira milyan 26. Ganin cewa jihar Zamfara tana daga cikin jahohin arewa da suke fama da matsanancin yunwa, rashin tsaro, kashe-kashe da sace-sace.

Mutane sun yi ta rubutu da kafawa gwamnan hujja da wasu zantuka da ya yi a baya wanda yake magana akan dalilan da suke haifar da rikice-rikice a jihar tashi tsawon shekaru. Wasu suna ganin hakan yanada nasaba da siyaya musamman lokacin da yarage kasa da wata guda kafin fara harkokin siyasa.

Ko yaya kuke kallon wannan lamarin?
Rariya.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post