Maganin Ciwon Mara Lokacin Al'ada

MAGANIN CIWON MARA LOKACIN AL'ADA :



Ciwon mara lokacin Al'ada, abu ne dake
damun Mata da yawa. Amma ga wasu
fa'idodi nan ku jarraba. In sha Allahu za'a
samu dacewa.
1. A samu Tsohuwar Tsamiya a jika aruwa
tare da bushashiyar gauta arika shan ruwan
tun kwana biyu kafin zuwa haila, har lokacin
da hailar zata fara zuba. Wannan Mataye da
dama sun jarraba kuma sun dace.
2. MAN ZAITUN : A Karanta ayoyin Alqur'ani
acikinsa sannan Mace ta rika shan cokali
guda safe da yamma kullum har zuwa
lokacin zuwan Jinin al'adarta. Kuma zata rika
shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda
al'aurarta saboda ayoyin da aka tofa).
Shima wannan idan anyi shi za'a dace. Koda
Aljanu ne suke rike mata Marar, ko suke
sanya mata ciwon jikin to zata samu
waraka.
3. KUSTUL HINDI : Idan an jikashi a ruwa ana
shansa safe da yamma shima yakan
Magance matsalar ciwon mara ko rashin
zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin
Al'ada.
Kuma koda ajiyar Aljanu ne a marar mace ko
mahaifarta, in sha Allahu zata samu waraka.
Da fatan Allah shi amshi dukkan abinda
muke roka ma junanmu. Nagode
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post