Ga tikitin shiga dajin sambisa》Zuwa Gudaji Kazaure


A kwanakin baya dan Majalisar Wakilai Muhammad Gudaji Kazaure  ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Da ya sahale masa shiga Dajin Sambisa a matsayinsa na tsohon mafarauci domin yakar Boko Haram. 



Idan har yanzu yana da muradin bayar da wannan gudunmawa, ga dama ta samu. Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya dauki mafarauta 500 domin taimakawa sojoji yaki da Boko Haram. 

Ina mai ba ka shawara da ka yi amfani da wannan dama domin shiga cikin 'yan uwanka mafarauta zuwa Dajin Sambisa.
Daga Maje El-Hajeej Hotoro.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post