Ganduje:Abun da ya hanani zuwa muhawarar da bbc ta hada

GandujeHakkin mallakar hotoS T YAKASAI
Gwamnan Jihar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilinsa na rashin halartar muhawarar da sashen Hausa na BBC ya shirya a ranar Asabar a Kano da ke arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben gwamnan ya fitar, kwamitin ya bayyana cewa muhawarar ta ci karo da yakin neman zaben gwamnan da aka tsara tun tuni.
Sanarwar wadda shugaban kwamitin yada labarai na yakin neman zabe, wanda kuma shi ne kwamishinan watsa labarai a jihar Malam Muhammad Garba ya sa wa hannu, ta bayyana cewa gwamnan ya dakatar da duk wasu al'amura a wajen Kano domin mayar da hankali da ganawa da masu zabe.
Sanarwar ta ce: ''Ko da Gwamna Ganduje zai je muhawarar, zai je ne domin bayyana irin ayyukan da ya gudanar tun daga hawan sa karagar mulki sai kuma alkwawuran da zai yi idan an kara zaben sa, kuma abinda yake yi dama kenan a yakin neman zabe a sassan jihar.''
Sanarwar ta kuma kara da cea ''gwamnan dake bisa karagar mulki kuma ya sake tsayawa takara, ayyukansa a bayyane suke, ba sai ya fito ya bayyana su ba domin za su bayyana kansu.''
Kazalika ta kara cewa gwamnan ya so ya halarci muhawarar amma abubuwa sun yi masa yawa, mutane da dama suna jiran su hadu da shi a wurin yakin neman zabe.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post