An jefi shugaban AP Adams Oshionhole a Ogun

Shugabn jam'iyyar APC ta Najeriya Adams OshionholeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionShugabn jam'iyyar APC ta Najeriya Adams Oshionhole
An jefi shugabn jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshionhole a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke gangamin zabensa a birnin Abeokuta na jihar Ogun a jiya Litinin

An jefi shugabn jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshionhole a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke gangamin zabensa a birnin Abeokuta na jihar Ogun a jiya Litinin.
Abubuwa sun rincabe a wajen wannnan gangamin ne bayan da shugaban jam'iyyar ya ambaci sunan dan takarar mukamin gwamna na jam'iyyar ta APC a jihar, Mista Dapo Abiodun a lokacin da yake yin jawabi ga jama'ar da ta halarci taron.
Suna jin sunan Mista Abiodun daga bakin shugaban APCn sai jama'a suka fara yi wa Mista Oshiomhole ihu har wasu ma suka rika fifansa da abubuwa daban daban a filin wasa
A daidai lokacin ne gwamnan jihar Mista Ibikunle Amosun, wanda ke goyon bayan wani dan takarar na daban da ke jam'iyyar APM ya tashi ya roli mutane su kwantar da hankalinsu saboda kar su kunyata sa a gaban shugaba Muhammadu Buhari, kamar yadda ya ce.
Har sai da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya lallashi jama'a kafin suka natsu a wajen gangamin.
Daga nan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasa jawabin, amma bayan da ya daga hannun dan takarar jam'iyyar ta APC sai mutane suka sake fusata har suka cigaba da jifar tawagar shugaban.
Lamarin ya kai sai da jam'ian tsaro suka rika kare shugaban kasar daga masu jifa kafin a karkare taron.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post