Ofishin INEC ya yi gobara

Hukumar ZabeHakkin mallakar hotoINEC
Image captionDuka kayayyakin zaben dake karamar hukumar Qua'an Pan dake jihar Filato ne suka kone
An kona daya daga cikin ofishin hukumar zabe a Najeriya kwanaki shida kacal kafin gudanar da babban zabe a kasar.
Gobarar dai ta faru ne a ofishin hukumar a jihar Filato dake arewacin kasar inda muhimman kayayyakin zabe kamar akwatuna da takardun jefa kuri'a suka kone.
Mai magana da yawun hukumar ya bayyana kona ofishin a matsayin mayar da hannun agogo baya a bangaren shirye-shiryen zabe
A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar ta bayyana cewa wannan ne karo na biyu da aka samu konewar ofishinta a cikin wannan watan, inda tayi kira ga jami'an tsaro a kasar da su kara matsa kaimi wajen ba ofisoshinsu tsaro.
Ana sa ran dai za a gudanar da babban zabe a kasar a ranar Asabar.
A ranar lahadi ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi gargadi a kan magudin zabe.
A wani bangaren kuma, shugaban ya koka a kan zargin da hukmar EFCC a kasar tayi na makudan kudaden da ake fitarwa ba bisa ka'ida ba domin siyan kuri'a.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post