Shugaba Buhari ya daga hannun gwamna Ganduje ya bukaci a zabeshi karo na biyu

Shugaba Buhari ya daga hannun gwamna Ganduje ya bukaci a zabeshi karo na biyu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya daga hannun gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a wajan yakin neman zaben da yaje yi jihar inda, ya bukaci da a sake zabenshi a matsayin gwamnan jihar Kano.



Gwamna Ganduje dai yana cikin wata kwamacalar karbar kudin da aka ganshi a cikin wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa bidiyon da ya dauki hankula sosai a kasarnan.

Gwamnan dai ya musanta cewa ba shine a bidiyon ba, siddabarun zamani aka yi amfani dashi wajan hada bidiyon.

Sannan gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari nada muradu uku da take yakin neman zabe dasu, samar da tsaro, yaki da rashawa, da kuma habbaka tattalin arziki.

Shugaban jam'iyyar APC dai, Adams Oshiomhole ya taba bayyana cewa duk laifin da dan siyasa yayi idan ya koma jam'iyyar ta APC to an yafe mai laifin, kalaman shugaba Buhari yayi gum akansu.





Post a Comment (0)
Previous Post Next Post