Ko Buhari zai daga hannun Ganduje a ziyararsa ta Kano? 31 Janairu 2019

Shugaba Muhammadu Buhari
A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar yakin neman zabe jihar Kano.
Zuwan Buhari Kano don yakin neman zabe, ya zo da takaddama a tsakanin 'yan siyasa da sauran al'umma a ciki da wajen jihar, musamman bisa la'akari da hotunan bidiyon, da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa

Duk da dumbin muhimmancin wannan ziyara ga shugaban kasar da ma gwamnan jihar na nuna wa abokan adawa karfin farin jinin da suke da shi a jihar wadda ta kasance mai yawan jama'a a kasar, takaddama da ce-ce-ku-ce, sun zamewa zuwan shugaban kasar wani tarnaki.
Magoya bayan gwamnan jihar, na fatan cewa wannan ziyara ta shugaba Buhari, za ta kawo karshen rade-radin tsamin dangantakar da ake zargi ta shiga tsakanin Ganduje da Buhari.
Wasu dai na cewa wai shugaban kasar a yanzu, baya ma son hada hanya da 
Wannan dambarwa dai ta taso ne watanni hudu da suka shude a lokacin da aka fara kwaza labarin cewa an dauki hotunan gwamnan na Kano na karbar cin hanci daga hannun 'yan kwangila, kafin daga bisani jaridar Daily Nigerian ta fitar da wasu hotunan bidiyon da suka nannaga wannan zargi.
Gwamnatin jihar Kano dai ta musanta wannan zargi, inda daga bisani ma ta shigar da dan jaridar da ya wallafa bidiyon a kotu.
Duk da wannan dambarwa, akwai dumbin magoya bayan shugaban kasar da suke maraba da zuwansa, wasun su ma domin su ji inda gwamnatinsa ta kwana game da wannan zargi da ake yi wa gwamnan na jihar Kano.
Wani daga cikin magoya bayan shugaban kasar ya shaida wa BBC cewa' Talakawa sun zuba ido su gani ko mai girma shugaban kasa idan ya zo jihar Kanon, zai daga hannun gwamna Ganduje ko kuma akasin haka'.
Wannan batu na karbar goro da ake zargin gwamnan na Kano, shi kowa ke jira ya ji matsayin shugaban kasar a kai.
A bangaren 'yan adawa a jihar kuwa, cewa suka yi su sam ba sa maraba da wannan ziyara ta shugaban kasar.
'Yan adawan sun shaida wa BBC cewa, su fa ba sa farin ciki da wannan ziyara domin kuwa ba bu abin da shugaba Buharin ya yi wa jihar Kano sai gidan 'Kurkuku'.
Zuwan shugaba Buhari jihar Kano dai ya bijiro da dumbin tambayoyi da suka hada:
  • Ko idan ya zo zai daga hannun gwamna Ganduje, idan ya daga hannun na sa ina makomar kimar shugaban?
  • Shin ko ziyarar shugaban kasar za ta kawo mafita ga zarge-zargen cin hancin Ganduje?
Sanin amsoshin wadannan tambayoyin, sai an ga abubuwan da suka biyo baya bayan zuwan Buhari Kanon
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post