Idan dai kunji dadin mulkin Buhari to ku sake zabenshi>>Atiku

Idan dai kunji dadin mulkin Buhari to ku sake zabenshi>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci 'yan Najeriya dasu sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zabe me zuwa muddin dai sun ji dadin mulkin na Buhari.



Atikun ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta hannun me magana da yawunshi, Phrank Shuaibu inda yace, a duk fadin Duniya babu inda ake samun shugaban kasa da bai tabuka abin arziki ga 'yan kasa ba amma kuma ya fito yana so a sake zabarshi.

Yace shugaba Buhari kara saka Najeriya yayi cikin matsala a mulkinshi kuma kasashen Duniya dama 'yan Najeriya sun yi ittifakin cewa bazai ci zaben da za'a yi ba saboda 'yan Najeriya sama da miliyan dari basa iya cin abinci koda sau daya a rana dan haka suna cikin yunwa kuma suna fushi dashi, ba zasu saka mishi kuri'a ba.

Vanguard ta ruwaito cewa, Atikun ya kara da cewa,  ga duk wanda yasan ya samu aikin yi a karkashin gwamnatin Buhari to ya zabi Buharin wanda kuwa yasan ya rasa aikin yi ko kuma wani nashi ya rasa aikin yi ko kuma kasuwancinshi ya durkushe to ya fito ya zabi Atikun.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post