Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya

Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya

Kamfanin Facebook ya bayyana shirinsa na hade shafin da kuma Whatsapp da Instagram duka wuri daya.


Wannan zai bada dama ga masu amfani da shafukan daban-daban su rika zumunta ko tura sakwanni ko da kuwa mutum yana da rajista da manhaja daya zai iya zumunta da wadanda ke amfani da sauran.

Misali, idan mutum yana amfani da Facebook, sai abokinsa yana amfani da Instagram kadai, za su iya zumunci ko tura sako tsakaninsu.

Shafukan da ke zaman kansu, hadewarsu zai sa a rika tura sakwanni tsakaninsu.


Facebook dai shaidawa BBC cewa wannan shirin da sauran aiki a gaba domin yanzu aka fara.

Jaridar New York Times ce ta fara wallafa wannan labarin kuma ana sa ran cewa mai kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg ne ya fito da wannan sabon tsarin.

Kamar yadda jaridar ta New York times ta wallafa, an riga an fara wannan aikin kuma ana sa ran za a kamala shi zuwa karshen wannan shekara ko kuma farkon shekara mai zuwa.
BBChausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post