AN YAFEWA RAHAMA SADAU

Hukumar Tace Fina-finai Ta Yafe Wa Rahama Sadau


Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ta yafe wa fitacciyar jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau dukkan laifukan da ta yi, wadanda suka janyo aka hana ta yin fim.


Shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakalla, ya shaida cewa, "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".

Afakalla ya kara da cewa sun dauki wannan mataki ne bisa la'akari da gafarar da jarumar ta nemi a yi mata kwanakin baya.

A cewarsa, "Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta al'umar da take ciki.

"Don haka a matsayinmu na 'yan-Adam wadanda kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata.

Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi", in ji shi.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post