DA GASKE ZAINAB INDOMIE TA RASU???

Da Gaske Zainab Indomie Ta Rasu?



Jita-Jita dai bata karewa a yanar gizo, To wannan karon kuma jita-jitar ta  fa do kan jaruma  Zainab Abdullahi wadda akafi sa ni, da (Zainab indomie) jarumar tana cikin jerin 'Yan matan Hausa fim da tauraruwarsu ta Haska a lokacin baya, Jarumar wadda aka daina ganinta a Harkar fim shekara da shekaru da suka gabata, masoyanta Suka  daina ganin duriyarta kwata-kwata a Harkokin Fina-Finan Hausa.

Duk da cewar ta dakata da Harkar Fim. Amma hakan bai sa aka sha fa ma ta lafiya ba,  domin a kwana kin nan Ne akaita yada jita-jitar cewa ta Rasu.

Labarin jita-jitar rasuwa Na ta, ya fara yaduwa Ne a shafukan sada zumunta, Na yanar gizo irinsu: Facebook, da whataspp, Twitter, instgram da sauransu. Haka dai labarin Rasuwar Na ta, ya zagaye kafafen sadarwa Na yanar gizo wasu kuma sukaita kwafar labarin suna turawa Abokanansu, kowa yana tofa Albarkacin bakinsa, ba tare da sun tantace sahihanci labarin ba


Binciken Mu, ya nuna wannan dai ba shine karo Na farko da aka fara yada jita-jitar Rasuwar 'Yan Fim a yanar gizo ba, Domin mafi yawancin manyan jaruman da suka daukaka a masana'antar Hausa irinsu: Ali Nuhu, Adam A Zango, Sani Danja da Marigayi Rabilu Musa (Dan ibro) dukansu babu Wanda ba'a yada Jita-Jitar ya mutu ba, Allah ya jikan Dan Ibro, An Dade ana yada jita-jitar ya rasu tun kafin ya rasu, Amma bai Rasu ba, Sai da ya ida Iya adadin kwanakin da Allah ya tsara masa, Abun Nan ya Dade ya Na ci ma ni, tuwo a kwarya.

Sai kaga wasu don Rashin aikin yi, ko kuma Don San Ransu, kawai sun hau yanar gizo sun Rubuta karya sun tura, nan ne kuma wasu zasu kwafi labarin aita turawa har yaje Inda ba'a tsamanni.

Wakilinmu yaso jin ta bakin jarumar wadda ake zargin ta rasu, Amma abin ya ci tura, sai dai majiyarmu ta jiyo mana cewa jaruma tana garin Abuja, Inda can ta koma da zama, kuma tana cikin koshin lafiya.

Don haka ina kira ga 'Yan uwana musulmai masu irin wannan halin Na Rubutun karya a yanar gizo, da suji tsoron Allah Su daina. Domin Allah ya hanemu da yin karya, Allah ya sa Mu dace, idan kuma ajalinmu yazo Allah yasa Mu ci ka, da kyau da Imani. Amin

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post