PDP bazata taba yi maka fatan rashin lafiya ba – Makarfi ya fada ma Buhari


- Ahmed Makarfi ya ce jam'iyyar PDP bazata taba yi ma shugaba Buhari fatan rashin lafiya ba
- Ya ce adawa ba hauka bane
- Makarfi ya fadi hakan ne a zantawa da Shugaba Buhari yayi da shuwagabannin APC da PDP a fadar sa
Shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi, ya fada wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar juma’a 25 ga watan Agusta cewa, jam’iyyar adawa bazata yi wa shugaban mugun fata ba.
A yayinda yake wa shugaba Buhari murnar samun lafiya, Shugaban PDP ya roki Allah ya kara wa shugaban karfin gwiwa domin ya zartar da shugabanci da cigaba a kasar.
Makarfi ya fadi hakan ne a zantawa da Shugaba Buhari yayi da shuwagabannin APC da PDP a fadar shugaban kasa, Abuja.
Source:hausa.naij.com
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post