Hamshakin Attajirin nan, Aliko Dangote zai gina jami’ar kimiyya da fasaha a Abuja


Fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya kammala shiri tsaf na gina wata katafariyar jami’a a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Tsohon babban sakataren hukumar kula da jami’o’in Najeriya wanda shine shugaban kwamitin samar da jami’ar,Farfesa Julius Okojie ya bayyana cewar manufar kafa jami’ar ta Dangote shine don habbala ilimin kimiyya, bincike da kuma inganta tattalin arziki.
Farfesa Julius ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da kwamitin ta kai zuwa ga hukumar kula da jami’o’in Najeriya inda suka gana da babban sakataren hukumar, Farfesa Rasheed Abubakar.
A yayin ziyarar, har da shugabar gidauniyar Dangote, Zouera Yousouffou wanda ta bayyan cewa sun ware naira biliyan 200 don gina jami’ar, kuma tace za’a tabbatar da an samar da dukkanin abinda dalibai ke bukata a jami’ar don saukaka musu yanayin karatu.
A nasa jawabin, shugaban NUC, Farfesa Rasheed ya yaba da kokarin Dangote, sa’annan yayi alkawarin basu duk gudunmuwar da suke bukata, sai dai ya basu shawarar gara su gina jami’a ta gama gari, amma sai su baiwa bangaren ilimin kimiyya muhimmanci, ba wai jami’iar kimiyya kadai ba.
Da take nata jawabin, Zouera Youssouffou tace a shire suke su fara gina wannan jami’a, inda tace sun ware naira biliyan 200, ta kara da cewa tuni har sun sayi filin da za’a gina jami’ar a kai a Abuja.
© Naij
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post