- Tsohon shugaban kasar yace gwamnatinsa tab a al’ummar kasar cikakken yanci
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi sharhi a kan yunkurin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kafa dokar da zata haramta furta kalaman batanci ko nuna kiyayya a tsakanin mutanen kasar.
Tsohon shugaban kasar ya sake buga wani hoto a shafinsa na Facebook wanda ke dauke da rubutu kamar haka:
"Ni ne shugaban da aka fi zagi da suka a duniya, amma za a tuna da ni idan na bar mulki saboda cikakken 'yancin da gwamnatina ta ba alúmman kasar," kamar yadda sakon ya ce.