Kano: Gwamnatin jihar Kano za ta samar da wutar lantarki na hasken rana a kasuwar sabon gari a jihar


Gwamnatin jihar Kano za ta samar da wutar lantarki na hasken rana a kasuwar sabon gari da ke jihar
- Tawagar hukumar raya wutar lantarki a yankunan karkara sun ziyarci gwamna Ganduje a fadar gwamnatin jihar
- Ana sa ran za a kammala aikin a cikin watanni masu zuwa
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnati jihar tare da hadin gwiwar hukumar raya wutar lantarki a yankunan karkara a karkashin ma'aikatar wutar lantarki, ayyuka da gidaje don samar da wutar lantarki na hasken rana ga kasuwar sabon Gari da ke jihar.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan lokacin da ya karbi wakilai daga hukumar raya wutar lantarki a yankunan karkara a karkashin jagorancin babban darakta da kuma shugaban jami'in hukumar, Misis Damilola Ogunbiyi, wanda kuma ta na matsayin babban mataimakin na musamman kan harkokin wutar lantarki a ofishin mataimakin shugaban kasa.
Babban darektan harkokin yada labarai da sadarwa a fadar gwamnatin jihar, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa tawsagar sun ziyarci mai girma gwamnan jihar don sanar da shi ci gaban da aka samu, har zuwa yanzu, don tabbatar da aiwatar da wannan aikin, a cikin watanni, kamar yadda minista, mista Fashola ya umarta.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Dokta Abdullahi Umar Ganduje tare da tawagar hukumar raya wutar lantarki a yankunan karkara
source:hausa.naij.com
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post