kimiyar lantarki 1


GABATARWA
Masana da yawa sun bada maanar elekrostatic a matsayin tsayayyar lantarki maana lantarki mara motsi.
HALAYYAR SINADARAI
Masana kimiyar sinadarai suna fadin cewa matter kowanne abu ce dake dauke da nauyi kuma yake cin wuri,matter na dauke da kananan sinadarai guda uku.
Nafarko:proton mai dauke da chajin kari mai alamar (+) wanda a turance ake kira positive charge.
Nabiyu:electron shi kuma wannan yan dauke da chajin ragi mai dauke da alamar (-) wanda masana kimiyar lantarki suke kira da negative charge.
Na uku:wannan kalar shi kuma baida chaji kwata-kwata,wanda suka kirasa da neutron.
Idan anaso a yi wa wani abu chaji mai kari to ya zama dole acire chaji mai ragi daga cikinsa,haka kuma idan anaso ayiwa wani abu chaji mai ragi ya wajaba a cire masa chaji mai kara daga cikinsa.
.
.
.
.
KONDACTA,INSULETA DA KUMA SEMI-KONDACTA
Zamu iya rarraba abubuwa gida uku gwargwadan alaqarsu da wutar lantarki...
CONDUCTOR:wadannan sune abubuwan da suke barin cikakkiyar tafiyar chajin lantarki ta cikinsu..misalinsa shine karfe,graphite,jar waya.
Ta dayan 'bangaren kuma insulator sune wanda basa barin tafiyar chajin lantarki ta cikinsa,misalinsa shine katako,glashi dasauransu.sai kashi na uku wato semi conductor shi kuma wannan wani lokacin yana barin tafiyar chaji wani lokacin kuma baya barin tafiyar chajin lantarki,misalin wannan shine silikon da germanium...
Mu hadu a darasi na biyu,,,naku IBRAHIM AUWAL
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post