kimiyar lantarki 2


'KA'IDAR ELEKROSTATIC.
bincike ya nuna cewa abubuwa biyu masu chaji iri daya(misali (+) da (+) ko (-) da (-)) suna samar da force mai rabawa a tsakaninsu,ta daya bangaren kuma idan chajin ba iri daya bane ((+) da (- )) suna samarda force mai hadawa a tsakinsu.
Ga abun da manuniyar tace a harshen turanci:
"like charges repel,unlike charge attract"
ma'ana:chaji iri daya basa ga-maciji,chaji mabanbanta kuma suna haduwa.
HANYOYIN YIN CHAJI
akwai hanyoyi guda uku da ake yiwa wani abu chaji.
1.Chaji ta hanyar gogayya(charging by friction).
2.Chaji ta hanyar kusantarwa(charging by induction).
3.Chaji ta hanyar hadawa(charging by contact).
.
.
.
CHAJI TA HANYAR GOGAYYA:duk sanda aka goga abubuwa guda biyu,chaji mai ragi(electron) zai tashi daga abu guda daya zuwa dan uwan,wanda ya samu chaji mai ragi mai yawa ana kiransa da negatively charged particle,dayan kuma wanda chaji mai ragi ya ragu daga jikinsa ana kiransa da positively charge particle.
CHAJI TA HANYAR KUSANTARWA:wannan yana faruwa ne a lokacin da aka matso da abu mai chaji kusa da wani abu mara chaji,alokacin shima mara chajin zai samu chaji.
CHAJI TA HANYAR HADAWA:wannan shi kuma yana faruwa ne alokacin da wani abu mai chaji ya bada chaji zuwa wani abu mara chaji saboda an hadasu.
Naku IBRAHIM AUWAL
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post