Zan binciki dala biliyan 16 da Obasanjo ya kashe akan gyaran wutar lantarki>>Buhari



A yakin neman zaben da yayi jiya a jihar Bayelsa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tabbar da cewa zai binciki kudin gyaran wutar lantarki da aka kashe da suka kai dala biliyan 16 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Buhari yace duk da matsalar tsaro da ake fama da ita nan da can gwamnatinshi ta yi kokari wajan habbaka tattalin arzikin kasarnan ta yanda yanzu kasar ta kama hanyar dogaro da kanta.

Ya kara da cewa maganar kudin da aka kashe, dala biliyan 16 akan gyaran wutar lantarki, ku shaidane cewa, babu wutar babu kuma kudin, dan haka zamu binciki yanda aka yi da kudin kuma mu kwato su daga hannun wanda suka sace su.

Duk da cewa shugaba Buhari be ambaci sunan Obasanjo ba amma a lokacin mulkinshi na 1999 zuwa 2007 ne aka ruwaito cewa an kashe dala biliyan 16 akan gayarn wutar lantarki.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post