'Yan Najeriya na shirin kada kuri'a don zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.
Misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar agogon Najeriya ake sa ran bude rumfunan babban zaben wanda aka dage tsawon mako daya saboda matsaloli da suka shafi raba kayan zabe a sassan kasar.
'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben, amma Shugaba Muhammadu Buhari na APC mai shekara 76, da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP, mai shekara 72 ne suka fi jan hankali a zaben.