Buhari ya ce ba zai fadi zabe ba


Buhari ya ce ba zai fadi zabe ba
Ku latsa alamar lasifika domin sauraren muryar Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu makawa shi ne zai lashe zaben shugaban kasar.
Da yake amsa tambayar wakilin BBC kan ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce "ni zan ci zabe."
Shugaba Buhari ya kada kuri'arsa ce a birnin Daura da ke jihar Katsina tare ds mai dakinsa Aisha Buhari da rakiyar wasu jami'an gwamnatinsa.
Sai dai abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce a matsayinsa na mai kare mulkin dimokradiyya zai yi biyayya ga sakamakon zaben kasar.
Wasu hotuna sun nuna yadda Shugaba Buhari ya kada kuri'a inda ya zabi kansa.
Mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaran Reuters ya dauki hotunan takardun kada kuri'ar Buhari, wadanda suka nuna cewa ya zabi kansa.
BuhariHakkin mallakar hotoREUTERS
Hukumar zaben Najeriya dai tana ba da shawara kada masu kada kuri'a su bayyana wanda suka zaba, saboda hakan ya saba tsarin tarbiyyar dimokradiyya.

Hare-hare

Sa'o'i biyu kafin bude rumfunan zabe ranar Asabar, al'ummar Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun ce sun ji fashewar bama-bamai da harbe-harben bindiga.
A wata sanarwa, 'yan sandan jihar sun ce babu wata barazana ga jama'a. "Jami'an tsaro ne suka yi harbe-harben domin tauna tsakuwa," in ji sanarwar.
Jihar Borno dai ta kasance cibiyar mayakan Boko Haram wadda ta yi shirin ganin ba a gudanar da zaben ba.
Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rawaito cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ne sun kai hari garin Geidam, inda suka tilasta wa jama'ar garin ficewa daga garin.

Me ya sa aka dage zabe?

Sa'o'i biyar kafin bude rumfunan zabe ne dai a ranar Asabar ta 16 ga Fabrairu hukumar zaben Najeria ta sanar da dage zaben.
Hukumar ta bayar da dalilan da suka janyo dage zaben da suka hada da yunkurin yin magudi da rashin kai kayan aiki mazabu da kuma rashin kyawun yanayi.
Yanzu hukumar ta INEC ta ce ta shirya tsaf domin tafiyar da zaben.
Wannan Layi ne

Yadda zaben yake?

Duk dan takarar da ya samu kuri'un da suka fi yawa, idan dai har ya samu kaso 25 na kuri'un da aka kada a jihohi 24 daga jihohi 36 na kasar.
'Yan takara 73 ne suke neman kujerar shugabancin kasar amma fafatawar ta fi zafi tsakanin 'yan takarar jam'iyyu biyu.
Taken Jam'iyyar shugaba mai ci, Muhammadu Buhari shi ne 'Next Level' wato kai Najeriya zuwa matakin ci gaba.
Ita kuma jam'iyyar adawa ta PDP wadda tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar yake takara na da taken 'to get Nigeria working again', abin da ke nufin jam'iyyar za ta dawo wa najeriyar hayyacinta.
Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Buhari da lalata shekaru hudun da ya kwashe a kan karaga.
Dukkanin 'yan takarar guda biyu dai sun fito daga yankin arewacin kasar mai yawan musulmai. Kuma dukkanninsu sun wuce shekara 70 da haihuwa.

Matsalolin Najeriya

Najeriya ce dai kasa mafi girma a yawan jama'a da kuma yawan albarkatun man fetur. To sai dai rashawa da cin hanci da kuma gaza zuba rarar da ake samu daga sayar da man a kasuwar duniya ne ke tarnaki ga cigaban kasar.
A 2016, kasar ta samu komadar tattalin arziki. An kuma samu jan kafa kafin kasar ta samu ta farfado, al'amarin da ke nuni da cewa ba a samar da isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar da ke neman aiki ba.
Za a iya cewa kaso daya bisa hudu na matasan kasar ba su da abun yi.
Wannan Layi ne
Alkaluman masu zabe
•Yan takarar shugaban kasa guda 73
•Masu katin zabe miliyan 73
•Kaso 51 da masu kati 'yan kasa da shekara 35
•Akwai rumfunan zabe dubu 120a fadin kasar.
.......
BuhariHakkin mallakar hotoREUTERS
Shugaba Buhari ya ce ya murkushe kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, to sai dai har yanzu kungiyar na da karfi.
Sannan kuma ana ta yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar.
Najeriya dai ta fuskanci mulkin soji har zuwa 1999, duk da cewa an samu gwamnatocin dimokradiyya wadanda ba su yi tsawon rai ba kafin nan.
A bana kasar ke cika shekara 20 da dawo wa turbar dimokradiyya.
A 2015 ne aka zabi shugaba Buhari, lokacin da kasar ta kafa tarihi, inda dan takarar jam'iyyar adawa ya kayar da shugaba mai ci.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post