Shugaban kasar Amurka ya bukaci musulmar 'yar majalisa ta farko a kasar da ta sauka daga mukaminta

A ranar Lahadin da ta gabata, Omar ta yi zargi a shafinta na Twitter cewa, wata kungiyar da ke kare muradun Yahudawa a Amurka da kwamitin da ke kula da hulda da jama’a a majalisar, na bai wa ‘yan majalisar kudade, domin su rika goyon bayan kasar Isara’ila.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi kira ga sabuwar ‘yar majalisar wakilai Ihan Omar, wacce ‘yar Democrat ce, da ta yi murabus daga mukaminta.

Trump ya yi kiran ne bayan da ‘yan Democrat da ‘yar Republican suka yi ta sukar ta, kan wani tsokaci da ta yi, wanda aka ayyana shi a matsayin nuna kyama ga Yahudawa.

A jiya Talata shugaba Trump, ya fadawa manema labarai cewa, hakurin da Ilhan ta bayar “ya yi kadan” inda ya ce afuwar da ta nema ba ta kai har ga zuciyarta ba.

Ya kara da cewa, idan ba za ta yi murabus daga matsayinta na ‘yar majalisa ba, kamata ya yi ta sauka daga mukaminta na mamba a kwamitin majalisar, da ke kula da harkokin kasashen waje.

A ranar Lahadin da ta gabata, Omar ta yi zargi a shafinta na Twitter cewa, wata kungiyar da ke kare muradun Yahudawa a Amurka da kwamitin da ke kula da hulda da jama’a a majalisar, na bai wa ‘yan majalisar kudade, domin su rika goyon bayan kasar Isara’ila.

Amma a ranar Litinin Ilhan, ta fito ta ba da hakuri, bayan da ‘yan Republican da ‘yan Democrat suka yi ca a kanta.
VOAhausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post