Bayan hatsaniyar da ta faru a jihar Ogun lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yaje yakin neman zabe jihar, jiya, Litinin, wadda har ta kai ga aka jefeshi shi da shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, shugaban ya bukaci jama'ar jihar da su zabi dan takarar da suke so dan a samu zaman lafiya inda yace hakan damar da dimokradiyya ta basu ce, saidai jam'iyyar APC ta sha banban da ra'ayin na shugaban kasa.
Dailypost ta ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta fitar da sanarwar cewa gwamnan jihar, Ibikunle Amosun ne da gangan ya dauki hayar matasan da suka jefi tare da kunyata shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Dan haka suka bukaci jama'ar jihar da su zabi 'yan takarar jam'iyyar APC kawai a kowane mataki kuma bayan zabe jam'iyyar tasha alwashin daukar mataki akan gwamnan, saidai bata bayyana ko wane irin mataki zata dauka akan gwamnan ba.