Ofishin yaki neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi allawadai da matakin hukumar zaben kasar, INEC, na dage manyan zabuka.
Hukumar zaben ta ce ta dage zaben shugaban kasa daga ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa 23 ga watan na Fabrairu.
Kazalika za a gudanar da zaben gwamnoni ranar tara ga watan Maris maimakon ranar biyu ga watan na Maris.
Sai dai sanarwar da Mr Festus Keyamo, mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben shugaban Najeriya ya fitar ta zargi INEC da hada baki da jam'iyyar hamayya ta PDP domin magudin zabe.
"Muna fatan INEC za ta zama 'yar ba-ruwanmu a annan harka ta zabe domin kuwa jita-jitar da ake watsawa na cewa an dage zaben ne da hada bakin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, wacce da ma bata shirya shiga zaben ba," in ji Mr Keyamo.
Masu sharhi dai na ganin dage zaben zai janyo wa hukumar zaben bakin jini da kuma sanya shakku a zukatan 'yan Najeriya game da shirnta na gudanar da sahihin zabe.