INEC ta dage zaben shugaban Kasa Najeriya

Hukumar zaben ta Najeriya ta ce ta dage zaben ne zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.
Da yake sanar da matsayin hukumar ranar Asabar da kusan asubahi, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni zuwa ranar tara ga watan Maris.
Farfesa Yakubu ya ce sun dauki matakin ne sakamakon matsalolin rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar a kan lokaci.
A cewarsa, "Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta gana ranar Juma'a, 15 ga watan Fabrairu inda ta sake nazari kan shiriye-shiryenta na zaben shekarar 2019, don haka an dage zaben da za a yi ranar Asabar 16 ga watan Fabairu zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Kazalika, za a gudanar da zaben gwamnoni ranar biyu ga watan Maris."
BBC HAUSA
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post