Tsoshon shugaban jam'iyyar PDP, Adamu Mu'azu ya koma APC
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Adamu Mu'azu ya bar jam'iyyar zuwa APC,
sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, Yayanuwa
Zainabari ya tabbatar da wannan batu ga manema labarai.
Dailypost ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban jam'iyyar PDP yankin
Arewa, Alhaji Babayo Garba Gamawa da tsohon sakataren gwamnatin
tarayya, Alhaji Ahmed Yayale, da kuma Alhaji Kaulaha Aliyu na daga cikin
wanda suka fice daga PDP zuwa APC.
Ya kara da cewa, wannan ficewa ta manyan jam'iyyar ya matukar kada su amma wannan ba zai hana PDP lashe zabuka masu zuwa ba.
Ya kuma ce babban dalilin ficewar wadannan manyan jam'iyyar nasu zuwa APC shine dan su gujewa kamun hukumomin EFCC da ICPC.