Messi da Suarez sun ci kwallaye fiye da na Madrid

Messi da Suarez sun ci kwallaye fiye da na Madrid

Barcelona ta fara gasar La Liga a shekarar 2019 da kafar dama, bayan da ta doke Getafe da ci 2-1 a ranar Lahadi, kuma Lionel Messi da Luis Suarez ne suka ci mata kwallayen.


Hakan ya sa Messi dan wasan tawagar Argentina yana da kwallaye 16 a La Ligar bana, shi kuwa Suarez ya ci 12, jumulla suna da 28 a wasannin da ake bugawa.
Kwallayen da 'yan wasan biyu suka ci sun haura wadan da Real Madrid ta zura a raga guda 26, Atletico Madrid ma 26 take da su.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post