Buhari ya mana abinda bamu ji dadi ba lokacin da ya zo gaisuwar mahaifinmu>>inji dan Shagari
Aminu Shagari, wanda da ne ga tsohon Shugaban Najeriya, Shehu Shagari,
ya bayyana rashin halascin da ya ce Buhari ya yi musu bayan rasuwar
mahaifin na su.
Ya yi wannan fallasa ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar PUNCH a ranar Lahadi.
Ya ce duk da mahaifin su ya gafarta wa wadanda suka cuce shi, amma bai
taba mantawa da cutar da suka yi masa ba. Ya na magana ne a kan yadda
Buhari a matsayin sa na babban jami’in soja, ya ci amanar shagari, har
ya hambarar da gwamnatin sa cikin 1983.
Shagari wanda ya yi shugabanci daga 1979 zuwa 1983, ya rasu ne a ranar 28 Ga Disamba, 2018, a daidai shakaru 93 a duniya.
Buhari ya je Sokoto a ranar 30 Ga Disamba, domin ya yi ta’aziyyar Shagari ga iyalan sa.
A cikin hirar da PUNCH ta buga a ranar Lahadi, an tambayi Aminu Shagari
shin wane darasi ya koya, ganin wanda ya yi wa mahaifin sa juyin mulki,
yace bai iya ba, amma ya je ta’aziyya ya na yabon irin mulki da halayya
ta mahaifin na su, wato Shagari?
Aminu ya ce maganar gaskiya ba su ji dadin yadda Buhari ya nuna ba a lokacin ta’aziyyar da kuma kafin rasuwar sa.
“Har mahaifin mu ya rasu, wanda ya hambarad da shi bai sake ba shi wani
kulawa ko mutuntawa ba, duk kuwa da cewa bayan ya hambarad da shi, ya
bincike shi, amma bai kama shi da aifin komai ba.”
“Da farko dai bari na fara da cewa duk da mahaifin mu ya yafe wa wadanda
suka ci amanar sa, amma ka san babu yadda za a yi mutum ya manta irin
abin da aka yi masa.
“Mu din nan kankin kan mu mun nuna wa Buhari goyon baya. Amma tun daga
lokacin da ya zama shugaban kasa, ba zan ce akwai wani batu da ya taba
sa ya tuntube mu ba.
“Ai kamata ya yi a ce mutumin da yake makusanci na kwarai ga mahaifin mu
har ya yi masa juyin mulki, ya dan saurare su, ko ya dube mu da
mutunci.”
Ya kara da cewa ko ta’aziyyar da ya kai dama ba su yi tunanin wasu
kalamai na kirki na tausar da zukata za su fito daga bakin Buhari ba.
“Lokacin da ya shigo gidan mu, mun yi tsammanin jin wasu dadadan kalamai
daga bakin sa. Amma ba mu ji komai ba, saboda bai ce komai ba din. Mu
ka ba shi littafin da wadanda suka je ta’aziyya ke sa hannu, amma sai
kawai ya sa hannu kadai, ko sunan sa bai rubuta ba cikakke, sai ya kuma
rubuta ranar da ya je.
“Maganar gaskiya raina ya baci matuka da wannan dabi’a ta Buhari. A zato
na a matsayin sa na musulmi, ko addu’a sai ya yi, ya ce: Allah ya
gafarta masa, mu ma idan ta mu ta zo, Allah ya gafarta mana’. Wannan ne
ya sa rai na ya baci matuka da Buhari.” Inji Aminu Shagari.
Premiumtimeshausa.