Kalli yanda wata mata ke faffallawa jariri mari

Kalli yanda wata mata ke faffallawa jariri mari

Wasu mutanen dai tausayinsu da sauki, jariri irin wannan da ko Allah be dora mai alkalami ba ko laifin me yayi da zai cancanci wannan muzgunawa? Wani hoton bidiyo me tayar da hankali ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wata baiwar Allah na faffalawa jariri mari.



Hannun baiwar Allahn kawai ake gani a cikin bidiyon me dauke da Dayis ne ko kunshi? 

Tana dukan yaron, a yayin da ya fara kuka kuma sai ta rufe mai baki kamar zata kasheshi, wannan abu ya harzuka da dama daga cikin wanda suka kalli bidiyon inda aka rika kira da a yadashi da kyau ko za'a iya gano ko wacece.

Ba ma wai dukan da ta wa jaririn kadaine abin takaici ba, irin yanda bin ya mata dadi har ta dauki hoton bidiyo take watsawa Duniya. Allah shi kyauta.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post