Buhari yayi kokari amma bazai iya ci gaba ba ya je gida ya huta>>PDP

Buhari yayi kokari amma bazai iya ci gaba ba ya je gida ya huta>>PDP

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi kokari amma yanzu be da kuzarin ci gaba da mulki dan haka ya kamata ya je gida ya huta.



Shugaban jam'iyyar Uche Secondus ne ya bayyana haka a wajan yakin neman zaben jam'iyyar, jiya a Kaduna, Secondus yace sake zaben Buhari kamar baiwa wasu boyayyun mutanene dama su ci gaba da juya kasarnan yanda suka ga dama domin ba Buharin ne ke mulki ba.

Ya bukaci a zabi Atiku dan ya samar da ayyukan yi da kawar da yunwa.

Shima Atikun da yake jawabi yace, APC ta yi Alkawarin habbaka tattalin arzikin kasarnan lokacin da ta karbi Mulki amma ba'a gani a kasa ba sannan ta yi Alkawarin samar da tsaro amma duk gashinan sai kashe-kashe ake samu.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post