Buhari zai kashe naira biliyan 7.30 kan jiragen zirga-zirgar sa cikin 2019

Buhari zai kashe naira biliyan 7.30 kan jiragen zirga-zirgar sa cikin 2019

Gwamnatin Najeriya ta shirya kashe naira bilyan 7.30 wajen hada-hadar shan mai da kula da jiragen zirga-zirgar Shugaba Muhammadu Buhari a cikin shekarar 2019.


Wannan adadin makudan kudaden da aka yi shirin kashewa, su na kunshe ne a cikin bayanan kudaden da za a kashe wa Buhari domin zirga-zirga da jiragen saman sa a cikin gida da kuma kasashen waje a cikin 2019.

PREMIUM TIMES ta ci karo da waddanan bayanai daga Ofishin Kasafin Kudi na Gwamnatin Tarayya.

Wannan adadi na nuna cewa abin da jirgin Buhari zai lamushe a 2019, ya haura adadin da aka kashe a shekarar 2017 da kuma 2018.

Cikin kasafin da aka ware wa jiragen, har da batun sake kayan dafe-dafen abinci, sake inganta karfin internet da sauran su.

Jiragen Shugaban Kasa su ne jirage na biyu mafi yawa a Najeriya, bayan jiragen kamfanin Air Air.

Sannan kuma ana ta korafin yadda ake kashe makudan kudade a kan jirgin, fiye ma da lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Kafin bayan Buhari ya hau, bai dade ba ya ce ana kashe kudade a lokacin Jonathan kan kula da gyare-gyaren jiragen shugaban kasa, har ma ya yi alkawarin zai rage yawan su ta hanyar saida wasu.

A cikin watan Nuwamba 2015, akwai jiragen shugaban kasa har guda goma cur.

Sai dai kuma a lokacin, Kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu, ya bayyana cewa har yanzu ba a fasa saida jiragen ba, amma kuma ba za a sayen da su da farashi na tayin-wulakanci ba.

Har yau ba a kara jin labarin tashin zancen saida wani jirgi ko daya ba.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post