Ba sauran gidan haya:Kalli sabon gidan zamani da Hadiza Gabon ta gina
Wadannan hotunan sabon gidan tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabonne
da ta kammala ginawa, ta saka hoton gidan a dandalinta na sada zumunta
inda ta bayyana cewa babu sauran gidan haya.
Abokan arziki da dama sun ta tayata murna da fatan Alheri.
Tauraron mawakin Hausa, Nazifi Asnanic yayi takakkiya har gidan inda yaje tayata murna.
Muma muna tayata murna da fatan Allah ya sanya Alheri.
Kalli karin hotuna.