Yar Boko Part 2:Hausa Novels

Kwanan hira sukayi, tare d bawa juna labaran bayan
saduwa sai byn sallar asuba sannan suka Kwanta, marsie
ce t fara tashi ganin 10:00am yasa t d'ala musu duka
suka tashi firgigit, jiddace tace lfy? Tace goma tayi bccin y
isa haka, tsaki tayi tare d Mai d kai t Kwanta hakama
neenerh, ganin basuda niyyar tashi t nufi toilet tayi wanka t
shirya t sami mom a Kitchen d asabe house maid suna
hada abincin breakfast, tasa hannu suna hira har suka
Gama.
.
Komawarta daki keda wuya t taddasu shame shamr
akwance basuda niyyar tashi, aikuwa batayi yunkurin
tashinsuba, fridge t isa t dauko ruwan Swan mai sanyin
tsiya t kyalayawa kowacce a fuska habawa sai gasu a
zaune dingirgir, ganin Marsie ce, sukayo kanta, aikuwa t
zuba a guje t nufi kofa suka rufa mata baya, dakin Mom t
nufa, ganinta aguje Mom tace lfy kike gudu? Tare d
rukunkume mom din,Kanta rufe baki ganin su neenerh tai
Sun fado kamar daga sama, suna kokarin dukan marsie d
kyar Mom ta kwaceta bayan Sun doddoketa, mom tace
meye haka ai wannan wasan jakaine, ku bakusan kun
girma bane, jiddace t mayarwa da Mom abinda y faru, nan
t baiwa marsie rashin gaskiya tare d ja mata kunne karta
sake.
Kasancewar yau saturday tin karfe shabiyu suka bar gida,
kaya iri daya suka Sanya, tamkar taurari sai walwali suke
,kowa y gansu jiyake dama yayansane, haka suka
zazzaga gidajen yan uwan d abokan arziki karshe suka
yada zango gidan kakarsu yadikko basu suka dawo gidaba
sai magrib.
Washegari ma haka suka fuce, sabanin jiya, yau zaga gari
sukai tare d ziyartar guraren shakawata,karshe sukayo
shopping suka nufo gida cikin jindd, dalilin d yasa sukesan
zuwa kano kenan Mom n sakar musu kudi su wataya.
.
Yau take Monday, karfe tara suka shiga Gate din campus
din, sanye d abaya bakake, inka hangosu daga nesa kai
kace larabawa ne, daidai musa Abdullah auditorium tayi
parking suka futo, nan kallo y koma kansu,fitowarsu tayi
daidai d isowar malm haneef cikin schl ,wani daga cikin
student y aika yace y kira Mai neenerh, t sameshi a offc
dinshi,cikin sakanni dalibin y isar d sakon Malam g
neenerh hakan b karamin harzuka zuciyanta yayiba, haka
suka nufi office dinshi, isarsu keda wuya sukai knocking, y
basu ixinin shiga ,sallama sukai tare d shiga, risinawa
sukai tare d cewa good morning sir? Y amsa d morning,
ganinsu baki daya y sanyashi jin b dadi, yace n kiraki
Danna Karbi phone number dinki, idan akwai wani infrmtn
d nakesan isarwa gareku zanyi t hanyar yi miki text,wani
sanyi taji a ranka, dama fargabarta kada zargin su zuhra y
kasance gaskiya,d farincikinta t bashi numbr suka futo,
futowarsu keda wuya tayi dialling Numbr din zuhra, ringing
daya t dauka hade d sallama, tace kuna inane, zuhra t
amsa d ina hnya nan d 5mints xan iso, ummylolo t kira
tace Besty kin shigone t amsa d, already am in d lecture
Hall, katse wayar tayi suka nufi hall din, front seat Ummy
tayi nasarar samar musu danhaka suka zauna,sunyi
lectures Sun gama sabanin ranar friday yau su biyar suka
taho cikin farinciki d zolayar juna.
Kamar yanda Mlm haneef y umarci kb d neernh suyi sunyi,
a kwana atashi b wuya gobe ne t kama talata ranar d zaayi
presentation, neenerh n daya daga cikin grp leader's d
zasuyi presentation din.
.
Karfe biyu n rana Hall y cika makil ,har wadanda ma basa
zuwa lectures din yau sunxo sbda presentation ,Two n
bugawa y shigo ajin ,sanye d fararen kaya d bakin Space
a fuskarshi kaikace wani balarabe usul, bakin gashin
kansa y kwanta sai kyalli yake.
Take aji yayi tsit ,rana bata karya sai dai uwar diya taji
Kunya, Grp A Ya kira, sukafuto jiki a sanyaye suka tsaya
gaban Class, maimakon yayi kamar yanda ya tsara sai
yace nine zanzabi wanda zai presenting paper din, zare
idanuwa sukai d mmki fal ciki, nan yayi pointing at wani
Guy, sai Grp leader din yace sir nine Grp leader ai ,a
harzuke mlm hanif yace kaizaka gayan abinda y dace ko
nine zanyi deciding, nan dalibin yayi shiru ,wanda y
zabane y futo gaban stage shikuma malm y matsa gefe,
murya a sarke yayi bayani dai dai iyawarshi, dayazo full
stop saiya dakatar dashi y sake pointing at wani Member
din,sai yabawa sauran members n Class dama siyi musu
tanbayoyi ,da an jefo question saiya zabi wanda zai
amsa,ahaka harya gama dasu yabasu 10 marks out of 20.
Haka yayi ta kiran grps har akazo kan grp H Wanda yake
shine nasu neenerh ,neenerh y zaba tayi presentation, wit
caurage t futo tafara sharhi kanya farga harta kammala, b
karamin burgeshi tayiba, yanda take pronouncing words
tare d amfani d vocabulary,daidai d yan Class saida suka
tafa mata ji kake raf raf raf
.
Anyi musu tanbayoyi kamar sauran grps din, neenerh ce t
amsa most of d question, a ransa yace no wonder bbyn
nan take burgeni ashe yanda take beautiful haka take
brilliant, abinda y kara rudashi charisma dinta,t kara samun
mutsugunni n musamman a zuciyarshi.group din su
neenerh sunfi kowanne samun marks, sukeda 18 yayinda
nasu kB yakeda 17,a wannan presentation din neenerh tayi
suna a class dinsu ,bama ga yan department dinsuba
harma faculty dinsu wato social management sciences
,kowa so yake yayi muamala d ita. Guys Kuwa Sun fara
rushing akanta, kowa n miko kokon barar shi.
Kullum malm Hnf saiya kira Numbr neenerh amma inta
dauka sai yaki magana haka zata karaci sallamarta ko
Hello b amsa harta gaji t ajiye, d abun y isheta saitai
saving number din ko ankira bata answering hakan b
karamin dagawa haneef hnkli yayiba. Y tsiri Tura mata
lovely txt msgs ,ranar d ta fara gani dariya tayi tace Allah
sarki yanxu fa watakila wanine zai turawa budurwarshi yayi
missing number tafado numbr ta ,hakan yasa tai sending
msg din bck, amma saitaga wani sweet text din y Kara
shigowa, nan t tabbatar d gangan ake turowa.
Wasa farin girki, tin ana mata txt din once a kullum
hartakaiga y kai saubiyu y koma sau uku, abunna matukar
damunta, inta kira Numbr din kuma sai adauka ayi shiru,
karshe tayi deciding turamai sakon text dan Allah koma
waye y bar turo mata txt, bataso inba haka b zatai blocking
Numbr din amma bata canja zaniba.
.
Rannan tana kwance a lafiyayyen gadanta gefanta mug din
tea ne take jira yayi sanyi t kurbe misalin 7:30 taji Phone
dinta n ringing d kamar bazata daga ba, number tagani
wadda batasaniba, tayi answering ,a daya barin cikin
husky voice dinshi yayimata sallama, Wow jin daddadar
murya yasanyata lumshe ido tare d amsawa, y tanbyeta y
weekend? T bashi amsa d lfy, katse Mai hanzari tai t
hanyar tanbya pls dawa nake mgna? Adaya barin yace
haneef, tace oho sir barka d dare, y Kara amsawa d lfy
lau, y Kara d cewa ga number na, inda akwai wani
announcement danakeso zan sanar dake haka zalika inda
complain u can contact me tru dis No, ta amsa d OK sir,
nan sukai sallama y ajiye wayar, dadi kasheshi ji yake
tamkar tayi accepting request dinshi t gama, a wannan
dare yayi kwanan farinciki.
.
Tinda haneef y kirata sai y zamto kullum saiya kirata Da
daddare dansu gaisa, itakam taga b dalilun d zai dinga
damunta d waya d sunan gaisawa, saidai inda Wata
akasa, adaidai wannan yanayin ne Dad y dawo, murna
gun neenerh vaa magana kasancewar ita tamafi sakewa
taci karanta bbu babbaka idan Dad na gida, misalin
shabiyu y duro kasar driver ne d yar lele(dadys pet ) sukaje
daukoshi,aikuwa tana hangoshi t tafi aguje tayi hugging
nashi Tana oyoyo dadyna, nayi missing dinka shima cikin
farinciki yace mmna nima nayi kewarki sosai, riko
hannunta yayi suna tafe tana zuba Mai surutu kaikace Wata
teenager,kowa kallansu yake d masu yabawa d ma.su
alawadai d wanga sara t yahudu, direbsne biye dasu
abaya dauke d jakunkunan daddy.
Isarsu gida suka taradda mom anci gayu, tasanya wasu
hadaddun English wears riga d skirt, kaikace Wata
budurwa t dame angyara gashi anyi parking dinshi atsakiya
kaikace bata wice shekaru 25 ba, sallamar mijinnata d
diyartata yasa ta tafi d murna tayi hugging nashi kamar
yanda diyartashi tayi mishi, cikin zolaya yace daughta kalli
mom naki tayi kyau irin wannan daukan wanka haka
,neenerh tace Dad aikai akama just to make u happy
( nikam ayusha ina gefe ina hangen su, araina nace wani
abun sai yan boko, wato yar ma ce kawarsu)shi bature
yadauki yayansa kamar kawayenshi abokan rayuwarshi d
shawara.
-
Daki y shiga yayi wanka, sannan y futo yaci abinci,
neenerh ansamu guri sai zuba ake, jakarsa y umarceta t
dauko mishi, yace t bude aikuwa English Wears ne y sayo
musu, ita nata masu wando yayinda n Mom masu skirt sai
murna take,g Sweet's d chocolate d cookies iri iri, t bude
wannan t dandana t bude wancan, cikin shagwba tace
Dad kayima Mom magana tunda K tafi taki barina nasanya
kananun kaya naje schl wai lallai sai manyan kaya, mom y
kalla yace wifey kibar takurata mna, inasayo mata danta
sanya, har nawa yarinyar take d zaa hanata sawa, mom
dai tayi shiru batace komaiba.
Adaidai wannan lokacin phone din neenerh tayi ringing,
Numbr haneef t gani sai ta share ,mom n lura d ita, tace
danmeyasa zaa kiraki bazaki dagaba, wato kinfara kula
Samari ko, zaro dara -daran idanuwanta tayi tare d cewa
walhi mom b saurayina bane, lecturer dinmune may b msg
zai gayan n gayawa yan ajinmu, nan take ran mom y Kara
baci meya hadaki d lecturer, abinda muka turaki mkrnta kiyi
kenan, duk yawan yan ajin sai ke zaikarbi no dinki yace
zai dinga kira, to tinda take takenki kenan aure zaa miki
mu huta, nan idanuwanta sukayi kwal kwal tare d zubar
hawaye tace walhi Mom b saurayina bane.
.
Kuma nigaskiya banasan aure, hawaye shabe shabe a
fuskanta tana rokon Mom, Dad dai baisa musu bakiba sai
yanxu yace mmna abinda nakeso d ke kimaida hankali
akan karatunki, karatun d kike shine kadai abinda xan mutu
n barmiki d zakiji dadinsa ,duk yawan dukiyar d zan barmiki
Mai karewace, kinga ke kadai gareni shiyasa nake d burin
naga kinzamo professor, murmushi tayitare d cewa Insha
Allah dad zanzamo Mai cikama buri akowana hali, Ya Kara
d cewa ni aburinama banso kika dawo nigeria ba, naso
acan London Zaki hattama, amma just to pleased ur mom
yasa nabi shawarar ta ,shafa kanta yayi, yana gogemata
hawayen yace yawwa mmna shiyasa nake alfahari dake a
kullum.
.
Dama inasan tanbayarki wana country kikesan zuwa dan
hutun end of Year, azake tace Istanbul, Dad yace hba
mmna last tym can mukaje, kidai zabi wata kasar nazari t
shigayi sannan tace saudi arabiya d America dariya yayi
yace wato wayo zakimin, daya nace kixaba, hannunshi t
kamo tana pls daddy inasan yin umara t maulud sannan
sai mu wuce american dariya yayi irinta mnya yace mmna
kina burgeni duk d tafarkin d muka doraki n yin zurfaffan
karatu hakan baisanya kinyi watsi d addininmuba, Allah
yayi miki albarka,dad ne yace kuzauna cikin shiri kina
gama second semester exams zamu tafi, Mom d ke gefe
sai murmushi take, Ashe dai yar tata, d hankalinta, jira take
taji t fadi kasashen masu jan kunne ta dasa mata full stop
saikuma taji t hada d kasa Mai tsarki.
Kullum kan Dad y futa saiya leka dakin neenerh y tabbatar
sungaisa sannan zaifuta, haka d y dawo kiranta zai farayi
mmna mmna, ita kuma t taho aguje ta rungumeshi, tare d
karbar tsarabar d yayo mata, y saba mata tintana
kankanuwa indai zai dawo Da daddare saiya kawo mata
chocolate ko ice cream d sauran kayan kwalam d
makulashe inkuwa y mnta, Ya zamto lazim y Tura yaran
gidan y sayo mata wani abin, sunyi masifar Shakuwa
kobaya kasar saiya kira Sun gaisa akalla twice a Rana.
.
A kwana a tashi b wuya,yau neenerh suka hattama exams
cikin farinciki t iso gida tinda t futo daga mota t rankaya
aguje tana kiran mom,mom dake kitchen tace o ni yar nan
neenerh dai har yau vatai hankali b,after dress dake jikinta
t cire t nufi kitchen gun Mom tare d rungumeta tana cewa
mom I hv now became a lvl 200 students,rawa t fara,
mom cikin murmushi tace Allah yasa angama a Saa,t
amsa d amin,Tare suka karasa girkin tarbar Dady sannan
taje daki tayi wanka tare d sallar magrib .
.
WANE NE DADY
.
.Asalin Dady sunan shi Muhammad anhaifeshi a garin
Rano dake jihar kano,mahaifinshi Wanda akafi Sani d
alhaji yelwa,alhaji yelwa ya kasance bafulatani mutum ne
mai tarin shanu ,tumakai d raguna ,kaf kauyen Rano babu
mai tarin dukiyarshi,yanada matar aure guda daya wadda
akafi Sani d habiba,sunada yara biyar,Hudu mata ,daya
namiji Wanda shine Muhammad ,tin tasowarshi mahaifinshi
ya so y koya mishi harkar kiwo ,koda babushi a doran
kasa yasan zai tafiyar mai d dukiya tamkar yana Raye,y
kuma kula d kannasa mata, kullum tunanin malam yelwa
baya wuce n y'ay'a matan d Allah y bashi ,yana kaunarsu
tare d tausaya musu,duk yanda yaso tilon danshi y gajeshi
hakan y faskara,Dan kuwa shi Muhd baida raayin kiwo
karatu y sanya agaba,ganin hanklin dannashi yafi karkata
ga Neman ilimi yasanya malam yelwa yimai fatan alkhairi a
abinda y sanya a gaba,kullum mal yelwa suka zauna hira
d dannashi b abinda yake kokarin dorashi akai illa kaunar
yan uwanshi mata,tare d nuna masa rauninsu,masu bukatar
taimakone,tare d yimai gargadin y kula d zumunci d kula
dasu a kowana hali,ganin haka watarana yace d
mahaifinnasa malam insha Allah zanrikesu hannu bibiyu
tare d jibantan alamuransu akowana yanayi n rayuwa,nan
mahaifinasa ya shiga Sakai albarka
Akwana atashi b wuya ,har Muhd y kammala makarantar
secondary dake garinsu ,cikin nasara yasamu gurbin
karatun aikin lauya a jamiar Bayero,farinciki kamar y zuba
ruwa akasa yasha,isarsa gida y Sanar d mahaifinsa d yan
uwanshi,ganin murnar d yake yasa suka tayashi,duk d
sudai basu gane ainahin abinda yake yiwa murnarba.
Cikin SAA d adduoin iyaye y kammala karatunshi ,yaje
makarantar law school dake garin ikko,anan y samu
shaidar zamowa cikakken lawyer kamar yanda kowana
lawyer yake alfahari.
Yadawo gida cikin farinciki, bai rufe wata
dayaba,gwamnatun jahar kano tabukaci matasa yan asalin
kananan hukumomunta dake d shaidar zama lauyoyi su
mika takardunsu Dan samun gurbin cigaba /zirfafa
karatunsu akasashen ketare,Muhd n daya saga cikin
matasan d suka samu nasarar tafiya jamiar dake cyprup
danyin karatun digiri n biyu wato masters.
.
Muhd n daya daga cikin daliban d sukafi sauran
hazaka,Dan haka hukumar makarantar ta bukacesu d suyi
mata aiki n tsawan shekaru goma,d kamar yaki amincewa
amma d ya tuna nauyin iyayenshi d yan uwanshi mata d
mahaifinshi ke jaddada mishi har kullum sai ya amince,sun
daukeshi a matsayin lecturer,sun bashi hutun wata daya
Dan zuwa gida nageria yayi sallama d yan uwanshi d
mahaifinshi, akwana atashi b wuya gobene Muhd zai koma
cyprus ,a wannan ranar y saiwa mahaifinshi wayar tafi d
gidanka,tare d sanya mishi simcard Dan ya dingajin
lafiyarsu,washegari sukai sallama y tari motar dazata
danganashi d Aminu kano airport dake kano,batare d bats
lokaciba suka dare jirgi suka Lula sararin samaniya
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post