'Yansanda sun kama shugaban Boko Haram

'Yansanda sun kama shugaban Boko Haram

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ta kama wani babban jigo a kungiyar Boko Haram a jihar Lagos dake kudu maso yammacin kasar.


Runduna ta musamman dake karkashin babban sufeto na 'yan sandan kasar ne suka damke shi.

Umar ne ake zargi da kai harin a unguwannin Kuje da Nyanya dake Abuja a 2015.

Haka kuma, ana zarginsa da jagorantar wani fashi da makami da ya faru inda aka kashe 'yan sanda 15 a unguwannin Galadimawa da Lugbe da Gwagwalada a Abuja.

Rundunar ta bayyana cewa Umar ya tsere ne daga Abuja mako biyu da suka wuce bayan wata arangama da yayi da jami'an 'yan sanda inda ya tsira da raunuka.

Bayan wannan arangama ne, jami'an suka kama mutum 4 wadanda ake zargin suna da alaka da dan bindigar, inda aka gano bindiga kirar AK-47 guda 4.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin, shi ya shirya harin da aka kai a bankuna a jihohin Edo da kuma Ondo a Najeriya.

Kuma shine kwamandan da ake zargin ya jagoranci kashe-kashen da akayi a hanyar Okene da kuma Kogi a Najeriya.

Wasu majiyoyi dai sun kara shaida cewa, Umar ne ya jagoranci kai hari da aka yi a gidan yarin da ke Jihar Neja a Najeriya a farkon shekarar nan kuma a wurin wannan harin ne ya rasa ido daya.

Haka kuma, a lokacin harin ne dai 'yan bursuna sama da 100 suka gudu.

Abba kyari, wanda shine jami'in dan sanda da ya jagoranci wannan samamen, ya bayyana a cikin jin dadi cewa, "yau dai ranar farin ciki ce a rayuwa ta, na jinjina wa 'yan sandan Najeriya."

"Na jinjina wa babban sufeto na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris kuma na jinjina wa Runduna ta musamman dake karkashinsa."
BBChausa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post