Yadda Kasafin Kudi Ya Kwana Na 2019 Daga Shugaban Kasa Muhammad Buhari


KASAFIN 2019: Irin nasarorin da muka samu – Buhari A dogon jawabin sa da ya gabatar a zauren zaman gambizar Mambobin Majalisar Tarayya da ta Dattawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da kalubalen da gwamnatin sa ta fuskanta a cikin gida da
wajen Najeriya, wadannan ba su hana mulkin sa ya samar da gagarimar nasara a fannoni daban-daban a tsawon shekaru uku da rabi da ya yi a kan mulki ba.

Ya bayyana musu cewa ya yi waiwayen tunatar da jama’a ayyuka da nasarorin da ya samu ne, sanoda wannan kasafin da ya gabatar shi ne na karshe a wannan zango na wa’adin mulkin sa. 

MUN WANKE NAJERIYA DA RUWA CIKIN COKALI

Buhari ya yi bayanin cewa gwamnatin sa ta yi rawar gani matuka wajen fitar da kasar nan daga kangin matsin tattalin arziki da ta rufta.

 Sannan kuma gwamnatin sa ta yi amfani da dukiya mai karanci matuka wajen gudanar da bimbin ayyukan nasarori a
fannin gona da inganta noma, samar da ababen inganta rayuwa da kuma tallafa wa masu kananan karfi a fannonin inganta rayuwa daban-daban.

Ta wannan bangare ne ya ce gwamnatin tarayya a karkashin sa ta rika tallafa wa jama’a ta hanyar amfani da kudade ta na tsamo jihohin kasar nan baki dayan su
wajen agaza musu da kudaden da suka rika biyan dubban ma’aikata albashi da kudaden alawus.

JAMI’AN TSARON MU NE BARGON LULLUBAR MU
Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa sojojin Najeriya bisa gagagrimar rawar da suka taka wajen samar da tsaro da dakile ta’addanci a fadin kasar nan.

Ya kuma yaba da irin sadaukar darayukan da suke yi wajen ganin cewa sun kare lafiyar mu da dukoiyoyin mu da kuma rayukan mu. 


RAWAR GANIN MU WAJEN INGANTA TATTALIN ARZIKI


A cikin jawabin sa, Buhari ya yi karin haske dangane da irin gagarimar nasara ko nasarorin da ya ce gwamnatin sa ta samar wajen inganta tattalin arziki. 

Ya ce kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida sun karu daga kashi 1.17 a karshen 2017 zuwa kashi 1.81 yanzu karshen 2018.

Latitar Najiriya a kasashen ketare kuma ta karu daga dala bilyan 28.57 a 2015 zuwa dala bilyan 42.98 a tsakiyar Disamba da muke ciki a 2018
.
Buhari ya ce an samu nasarar raguwar matsin fatara da tsadar kayan tasirifin rayuwa daga kashi 18.72 a 2017 zuwa 11.28 a cikin 2018. 

RAYUWA SAI DA RUWA
Buhari ya lissafa ayyukan samarwa da inganta ruwa a jihohi da dama da suka hada Bayelsa, Edo, Katsina, Taraba, wanda ya ce ana yi a Takum, Delta, Sokoto, Kaduna, Filato da kuma jihar Benuwai.

Ya kuma tabo nasarori a kan inganta zirga-zirga da hanyoyin jirgin kasa da ya ce an samar daga Abuja zuwa Kano, na cikin garin Abuja, Itakpe zuwa Ajaokuta
zuwa Warri da kuma Lagos zuwa Kano.

Ya ce ana kuma kara maida hankali da bada fifikon babban aikin titin jirgin kasa na Lagos zuwa Kano da kuma aikin katafariya kuma doguwar gadar Kogin Neja. 

TITINA: Buhari ya lissafa garuruwa sama da 50 wadanda ake gudanar da ayyukan gina titi na gwamnatin tarayya a fadin shiyyoyin kasar nan baki daya. 

GWAMNATIN MU TA KAWO HASKE, TA KAWAR DA DUHU
A bangaren hasken lantarki, Buhari ya bayyana irin nasarorin inganta hasken lantarki da makamashi da gwamnatin sa ta APC ta gudanar a fadin kasar nan.

Ya yi bayanin alfanun daukar ma’aikata a tsarin N- Power da y ace ya zuwa yanzu an dauki wadanda suka kammala karatun digiri na farko su 500,000 aiki.

CIYARWAR ’YAN FIRAMARE SU MILYAN 9
Sannan kuma ya bayyana adadin daliban firamare da ake ciyarwa su milyan 9,300,892 a cikin makarantu 49,837 a fadin cikin jihohi 24.

Ya ce ta wannan tsarin ne mutane 96,977 suka samu aiki. Buhari ya ce gwamnatin sa ta bayar da basussuka ga masu kananan kasuwanci har su milyan 1,78,804.

Ya ce ana tura wa gidaje 297,973 kudaden tallafi afadin kasar nan. 

Source: Hausatag.com.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post