Sai Da Muryata Ta Dashe Saboda 'Ihun Sai Buhari' Don Kare Martabar Buhari A Majalisa>>Honarabul Yaya Bauchi Tongo

Sai Da Muryata Ta Dashe Saboda 'Ihun Sai Buhari' Don Kare Martabar Buhari A Majalisa>>Honarabul Yaya Bauchi Tongo

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye dake jihar Gombe, Honarabul Yaya Bauchi Tongo na daga sahun gaba na wadanda suka yi kokarin karewa shugaban kasa Muhammadu Buhari martabarsa a majalisar tarayya a yayin da ya je gabatar da kasafin kudi a ranar Larabar da ta gabata, inda wasu daga cikin 'yan majalisu na jam'iyyar PDP suka dinga ihun ba sa yi tare da karyata shugaban kasa a yayin da yake jawabi.


A yayin hirarsa da RARIYA ta wayar tarho, Dan majalisar  ya bayyana cewa duk da yawan shekarunsa amma haka ya zage yana daga murya saboda kare martabar shugaba Buhari a yayin da wasu takwarorinsa 'yan majalisu ke neman ci wa shugaban kasan fuska a idon duniya.

Honarabul Tongo ya kuma bayyana dabi'ar da takwarorin nasa suka nunawa shugaban kasan a matsayin rashin tarbiya da kuma rashin da'a da girmama na gaba.

Dan majalisan ya kuma kara da cewa duk da irin wannan dabi'un da wasu daga cikin 'yan majalisun suka nunawa shugaban kasan hakan ba zai hana Buharin sake cin zabe ba a 2019 saboda al'ummar Nijeriya musamman talakawa suna tare da shi.

Yaya Tongo dai yana daga cikin 'yan siyasan da suka sake fitowa takara a zango na biyu, inda yake neman kujerar da yake kai a yanzu, wato kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye dake jihar Gombe.
Rariya.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post