Burodin Ayaba:Girke Girke

arkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin
koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin
ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma
don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda
muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku
nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a
zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga
da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar
cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu
da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa
hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu.
Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a
saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar,
sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha
ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana
sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post