KWANKWASO NE KADAI MADADIN BUHARI INJI APC

Tsohon Gwamna Na Kano ,Kwankwaso Shine Kadai zai Iya zama Madadin Shugaba Buhari Inji Mr John Odekina,  wani jigo Na jama'iyyar APC Na jahar Kogi.

Odekina wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Abuja, ya ce Kwankwaso yana da damar da zai ceci Najeriya daga mummunan halin da take ciki Na tattalin arziki.

A cewar Shi tsohon Gwamnan yana dabara wajan Iya mulki , Kuma Zai Iya amsa tambayoyin Yan jarida na kasar nan .

A matsayin sa na tsohon Gwamnan Ya Canza jahar Kano zuwa jahohi da akwai arziki a afrika ta hanyar bin tsarin sa.

"Yakamata Yan Nijeriya Su bawa Kwankwaso dama domin ya Canza tattalin arziki kasar zuwa na daya a afrika."  Ya ce .


Odekina ya bayyana gamsuwar cewa Sanata Kwankwaso zai magance matsalolin cikin Kasar da kuma samar da tsayayen wutar lantarki .

"Ya na da hangen nesa da kuma halayen jagoranci kuma zai bawa talakawa abunda suke buri mafarkin kasar ta zama "  odekina Ya kara cewa .


Za a tuna cewa Kwankwaso ya tsaya takara a zaben fidda gwani a APC a 2015 amma Bai samu yaci ba Sai aka fidda Shugaba Muhammad Buhari .
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post