AN KAMA BARAWON JJAMILA NAGUDU

Yan Sanda Sun Chafke Wani Mutum Da Ke Amfani Da Sunan Wata Jaruma Yana Bata Mata Suna.





Wani garsamemen kato ya fada komar jami'an tsaro a kano, bayan da ya bude shafin sada zumunta na facebook da sunan wata shahararriyar jarumar fina-finan hausa wato jamila umar nagudu, kuma ya rika amfani da shafin wajen ganin ya batawa jarumar suna.

Shi dai wannan mutum ya dade yana cin karensa babu babbaka, inda ya ke dora hotuna gami da kalamai da basu daceba da sunan jarumar, wanda hakan ke barazana ga mutuncinta.

Al'amarin ya kawo karshene bayan da wannan jarumi ya aikewa da wata mai suna Aisha daga katsina hotunan tsiraici, ya kuma nemi da idan har bata zo kano ta sameshi ba a matsayin shine jamila nagudu to zai yad'a hotunanta ya kuma bata mata suna wanda hakan ka iya jawo a koreta a makaranta, wannan barazana tayi tasiri akan yarinyar mai suna Aisha inda ba shiri ta hau mota zuwa kano domin bin umarnin wannan da ke mata barazanar ko su hadu ko ya bata mata suna.

Sai dai Alokacin da Aishar ta bayyanawa dan uwanta a kanon halin da take ciki, sai ya kai korafi hukumar 'yan sanda inda daga nan ne fa aka kafa tarko domin kama wannan jaruma, amma me? Maimakon jamila umar kawai sai ga wani garsamemen kato ya fada cikin komar ta 'yan sanda inda anan ne aka gano ashe gardi ne kawai yake Basaja da sunan mata kuma jarumar fim.

A halin da ake ciki dai, Jamila Umar ta bayyana farin cikinta da Allah ya tona asirin wannan azzalimi, inda tace hakika addu'arta ce ta fara ci, domin kuwa wannan gardi ya sha sanya ta cikin halin kaka na kayi.

To Allah ya kyauta ya kuma shiga tsakanin nagari da mugu.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post