A daidai irin wannan lokaci,sanyi ya fara kwankwasa kofa a wurare da dama. Da zarar an fara ganin hazo ko hunturo lallai wannan alama ce ta nuna cewa sanyi ya shigo. A wannan lokutan ne yakamata a fara takatsantsan wajen kulawa da fatar jiki. Idan ba’a kula da fatar ba, har sai da ta gama bushewa ko yin gautsi, hakan na daukan lokaci kafin a samu a magancesu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za’a magance matsalolin fata a lokacin sanyi. · Man kadanya; tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke da sinadarai masu warkar da cututtukan fata. · Kaushin fata; idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man ‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa man domin samun saukin lamarin. · Fason kafa; yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a kwanta a kullum domin samun saukin matsalar. · Sulbin fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska. · Karyewar gashi; kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko kuma man kwa-kwa na hana gashin kai zubewa.