Kungiyar Izala Tayi Gargadi Ga Rainin Wayon Da Akayi Wa Firdausi


Izala Tayi Gargadi kan Wasa Da Hakkokin Addini a Najeriya
Kungiyar tayi Allah wadai da Nuna tsangwama Ga Firdausi
akan sanya Hijabi
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jawo hankalin
hukumomi zuwaga wani labari da ya yadu akan wata daliba
musulma, mai suna Amasa Firdaos, wacce ta kammala
karatunta na zama lauya amma aka hanata samun shaida
saboda ta saka hijabi.
Sheikh Bala Lau yayi gargadin cewa addini baitaba zama
ginshiki ko mizani ba a tsarin gwamnatin Naijeriya. Saboda
haka, muna jawo hankalin mahukuntan kasar, malamai da
shuwagabanni da masu alhakin daukan ma'aikata ako wani
sashi da sauran jaami'an kasar da sukiyaye sanya banbancin
addini a matsayin mahangar duba cacanatar 'yan kasar a
kowane irin lamari musamman duba da yawan addinan dake
kasar.
Shugaban yaci gaba da cewa A yayinda muke kushe wannan
Al'amari danuna rashin dacewar sa, a gefe guda kuma muna
taya sauran 'yan Najeriya neman ayiwa wannar dalibar adalci
kuma a gurfanar da duk masu hannu a cikin wannan cin zarafi.
Muna kara jaddada kira ga hukumomi da 'yan kasar da suyi
koyi da sauran kasashen duniya domin wayewarsu takai har ga
kyale kowa yayi mu'amala gwargwadon yadda addininsa
yatanadar batareda tsageranciba ga dokokin ubangiji" Inji shi"
A karshe Muna tunatar da hukumomi cewa lokaci yayi da za'a
waiwayi karuwar rashin mutunta addini dayake aukuwa a baya
bayannan a najeriya, Shige gona da iri da yunkurin tozartarda
masu riko da addini Domin daukan matakin bai daya a kasar.
(C) JIBWIS Nigeria.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post