Wai Rahama Sadau Ta Dawo Kannywood Ne?

Da alama dai fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar
Kannywood wadda aka kora a da watau
Rahma Sadau ta shirya tarar rigima
bayan da tayi fatali da dukkan korar da
akayi mata sannan ta shirya sannan ta
kuma fito a matsayin jaruma a wani
sabon fim mai suna 'Dan Iya.'


Fim din dai kamar yadda muka samu
daga majiyar mu an shiyar kammala
shi sannan a kuma sake shi zuwa
kasuwa a watan Maris din shekara
mai zuwa ta 2018 sannan kuma
fitaccen mai bayar da umurnin nan
watau Yaseen Auwal ne ya bayar da
umurnin fim din.
NAIJ.com dai ta samu cewa fim din na
barkwanci ne kuma an shirya shi a
wani kauye ne da yake nuna rayuwar
manyan jarumai Rahma Sadau da
kuma Sadiq Sani Sadiq wanda shine
ya fito a matsayin dan iya din.
Sauran wadanda suka taka rawa a
shirin fim din sun hada da Rabi'u
Rikadawa, da kuma Aminu Sheriff
Momoh.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a
ranar 3 ga watan Oktobar bara ne dai
kungiyar masu shirya-fina-finan
Hausa shiyyar jihar Kano ta dakatar
da jarumar sakamakon wata waka da
tayi da ta sabawa addini da kuma
al'adar mutane
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post