Rikici Ya Kara Barkewa A Jam'iya PDP


- Baka raba PDP da takaddama da rikici
- Magagin faduwa zabe ne har yau bai sake ta ba?
- PDP ta lashi takobin dawowa mulki a 2019
Wani rikici ya barke a PDP
Ana ta samun baraka tun bayan da jam'iyyar ta PDP ta yi taron ta da zabuka na kasa, inda ake ta cece-kuce kan rikicin cikin gida na jam'iyyar, wasu har sun garzaya kotu.
To yanzu ma dai, rikici ne wanda Mista Emanuel Nwosu yake jagoranta, kan sai lallai an soke tare da sake zaukan da aka yi don cewa an tafka kura kurai da magudi.
Tun faduwar jam'iyyar zabe a 2015 take ta shiga halin ha'u'la'i da ma zarge zarge na tafka satar kudaden gwamnati kan mutanen ta da jami'ai.
Ya zuwa yanzu dai, jam'iyyar ta PDP bata sami nutsuwar da har zata iya wani katabus ba a zabuka masu zuwa.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post