Daga babansu baba
- Mun tattaro maganar Malamai
game da faduwar idi a ranar
Juma'a
- Wasu na ganin idan hakan ta
faru babu wajibcin zuwa Sallar
Juma'a
- Har wasu manyan Malaman ma
na ganin cewa Sallar Azahar ta
fadi
A daidai lokacin da ake shirin bikin
babban idi mun tattaro maganar
Malamai game da faduwar idi a ranar
Juma'a kamar yadda za ta kama
wannan karo daga wani darasi na
babban Malamin musulunci Sheikh
Muhammad Sani Rijiyar Lemu.
Jama'a wajen Sallar idi kwanaki
1. Magana ta farko
Malaman Malikiyyah sun tafi a kan
cewa dole ne ayi sallar Juma'a ko da
ta fadi a ranar idi don haka Allah
Madaukaki yayi umarni a Qurani
asali.
2. Magana ta biyu
Malaman Shafiiyah na ganin idan
hakan ta faru babu wajibcin zuwa
Sallar Juma'a ga wadanda su ka fito
daga kauyukan nesa amma mutanen
gari za su yi Juma'a.
3. Magana ta uku
Akwai 'yan mazhabar Hanabila da su
ka tafi akan cewa idan hakan ta faru
to sallar idi ta dauke Sallar Juma'a
gaba daya.
4. Magana ta hudu
Akwai Malamai irin su Imam
Shawkani da ke ganin idan Idi ya
fado a Juma'a to har sallar Azahar ta
fadi amma wannan magana na sa
akwai rauni.
Magana mafi inganci inji manyan
Malamai ita ce za a yi sallar idi
sannan kuma mustahabbi ne Liman
yayi sallar Juma'a ga masu niyya
amma ba dole bane don kuwa wata
idin ta dauke wata
- Mun tattaro maganar Malamai
game da faduwar idi a ranar
Juma'a
- Wasu na ganin idan hakan ta
faru babu wajibcin zuwa Sallar
Juma'a
- Har wasu manyan Malaman ma
na ganin cewa Sallar Azahar ta
fadi
A daidai lokacin da ake shirin bikin
babban idi mun tattaro maganar
Malamai game da faduwar idi a ranar
Juma'a kamar yadda za ta kama
wannan karo daga wani darasi na
babban Malamin musulunci Sheikh
Muhammad Sani Rijiyar Lemu.
Jama'a wajen Sallar idi kwanaki
1. Magana ta farko
Malaman Malikiyyah sun tafi a kan
cewa dole ne ayi sallar Juma'a ko da
ta fadi a ranar idi don haka Allah
Madaukaki yayi umarni a Qurani
asali.
2. Magana ta biyu
Malaman Shafiiyah na ganin idan
hakan ta faru babu wajibcin zuwa
Sallar Juma'a ga wadanda su ka fito
daga kauyukan nesa amma mutanen
gari za su yi Juma'a.
3. Magana ta uku
Akwai 'yan mazhabar Hanabila da su
ka tafi akan cewa idan hakan ta faru
to sallar idi ta dauke Sallar Juma'a
gaba daya.
4. Magana ta hudu
Akwai Malamai irin su Imam
Shawkani da ke ganin idan Idi ya
fado a Juma'a to har sallar Azahar ta
fadi amma wannan magana na sa
akwai rauni.
Magana mafi inganci inji manyan
Malamai ita ce za a yi sallar idi
sannan kuma mustahabbi ne Liman
yayi sallar Juma'a ga masu niyya
amma ba dole bane don kuwa wata
idin ta dauke wata