Akwai yiwuwar shahararren dan wasan Barcelona
Lionel Messi zai kaucewa daurin wata 21 a gidan
yari inda ya zabi ya biya tara, kamar yadda
rahotanni daga kasar Spain suka bayyana.
Wata kotu ce a Spain ta samu dan wasan da
laifin zambar haraji.
Babban mai gabatar da karar kasar zai
musanyawa Messi zaman gidan yari zuwa biyan
tarar euro 255,000 wato zai biya euro 400 a
kowace rana idan da zaman gidan kason zai yi.
Kotunan Spain ne suke da ikon yanke hukuncin
karshe game da batun.
ÆŠaurin shekara nawa za a yi wa Ronaldo, Messi
da Neymar?
An tabbatar da hukuncin daure Messi a gidan
yari
Ana zargin Ronaldo da ƙin biyan haraji
An samu Messi da mahaifinsa Jorge da laifin
zambar haraji a Spain fiye da euro miliyan hudu
tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.
An ci dan wasan tarar euro miliyan biyu,
mahaifinsu kuma euro miliyan daya da rabi.
A watan jiya ne kotun koli ta yi watsi da daukaka
karar da Messi ya yi.