No title

Barkanmu da warhaka tare da fatan ana lafiya.
Yaya shirin Sallah? Allah Ya nuna mana amin.
Sallah dai kamar kowace shekara an fi sanin mata
da dama da yin kunshi da kitso da dinkin kayan
Sallah da kuma sauran shirye-shirye. A yau ina
so in sake jawo hankalinku zuwa ga irin kwalliyar
da ya kamata a yi da Sallah domin idan akwai
wadda ba ta riga ta sayi lalle ba sai ta yi maza
ta saya. Yana da kyau a hada wannan kwalliyar
da dilke da kuma kurkum domin samun
ingantacciyar kwalliya.
• Yana da kyau idan an zo kwaba lalle sai a
kwaba shi da ruwan lemun tsami da sukari domin
ya kama da wuri. Za a iya yin kwalliyar lalle da
zanen fulawa a tafin hannu ko kuma a tafin kafa.
• Kurkum; kurkum na taimaka wa mace yin haske
amma an fi yawan amfani da shi ga amare a
lokacin aurensu. Amma kwalliya a yanzu ba sai
ranar auren mace ba, musamman ga masu aure
za su iya biya a yi musu kurkum a jikinsu domin
samun fata mai sulbi da santsi da kuma haske.
• Dilke; ana yin dilke ne kafin a yi kurkum. Domin
dilke na cire duk dattin da ke cikin fata tas yadda
fata za ta yi sumul da kuma sanya ta sheki.
• Kaya; Ana so a dinka kaya mai kyau sabo
wanda za a je Idi da shi ga wadda take da hali.
Akwai dinkuna masu kyau wadanda mace mai
aure za ta iya sanyawa a cikin gida domin burge
maigida. Idan ko za ta je masallaci sai ta sanya
hijabi don kada ta jawo hankali.
• Kitso: Idan za a iya yin hakuri, kananan kitso
sun fi kyau a kan fatar mace don haka yana da
kyau a samu wadda ta iya kitso ta zana kanana
kuma yadda za ta yi kyau.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post