Hukumar binciken sirri ta ta Najeriya DSS, ta
sanar da samun nasarar damke wasu ‘yan
ta’adda da ke shirya kai jerin hare hare a
garuruwan Sakkwato, Kano, Kaduna da kuma
Maiduguri, yayin da ake bukukuwan Sallah
karama.
Jami’an hukumar sun kame biyu daga cikin
wadanda ake zargin, Yusuf Adamu da
Abdumuminu Haladu da safiyar wannan Juma’a
a garin Sakkwato, kamar yadda jaridar Premium
Times da ake wallafata a Najeriya ta rawaito.
Cikin sanarwar da ya fitar a Juma’ar nan,
kakakin hukumar ta DSS Tony Opuiyo, ya ce tun
a makwannin da suka gabata suka samu
bayannan sirri da ke cewa, ‘yan ta’addan na
shirin kai hare haren bam a sassan Najeriya.
A ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki,
hukumar binciken sirrin ta kama wani kwararre
wajen hada bama bamai, mai suna Bashir
Mohammed a Shekar Madaki da ke karamar
hukumar Kumbotso jihar Kano.
Yayin gudanar da bincike kuma jami’an na DSS
sun gano manyan bindigogi kirar AK 47 guda
takwas, bindigogi masu sarrafa kansu 20, bama-
baman gurneti 27, sai kuma alburusai 793.
Zalika jami’an sun kwace tukunyar gas guda,
komfutar laptop 3, sai kuma, mota daya da
babur din hawa.