Masu iya magana na cewa siyasar Kano sai Kano, kuma a ko da yaushe ta kan zo da wani abu sabo, kamar yadda a bana salon Abba gida-gida da makamantansa suka hadu a yunkurin 'yan hamayya na kifar da jam'iyyar APC mai mulki.
Masu sharhi da dama sun yi hasashen Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai samu wa'adi na biyu cikin sauki ganin yadda rikici ya dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP da kuma tsagin Kwankwasiyya wadanda su ne manyan masu adawa da gwamnan karkashin jagorancin mutumin da ya gada Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Amma sai ga wankin hula ya kai APC da Ganduje dare, inda aka tafi zagaye na biyu, kuma PDP ta kasance a gaba da ratar kuri'a 26,655. Kafin daga bisani INEC ta bayyana APC a matsayin waccee ta lashe zagaye na biyun da tazarar kuri'a 8,982 jumulla. Masu sa'ido na gida da waje sun yi Allah-wadai da yadda karashen zaben ya gudana, inda suka ce an yi amfani da 'yan daba da jami'an tsaro wurin muzgunawa da hana 'yan adawa kada kuri'a, da kuma aringizon kuri'u, zargin da APC da INEC da 'yan sanda suka musanta.Sai dai jam'iyyar PDP ta ce za ta bi kadun batun a kotu, kuma masu iya magana na cewa shari'a kamar mace ce mai ciki wadda ba a san me za ta haifa ba sai an gani tukunna, a don haka komai zai iya faruwa.Ko ma dai ya ta kaya a kotun, a zahiri take cewa kawo yanzu Ganduje ya sha da kyar, abin da Hausawa ke cewa ya fi da "kyar aka kamani". Ga wasu daga cikin abubuwan da suka jawo wa gwamnan matsala a zaben har suka kai ga tasirin Abba K Yusuf da jam'iyyar PDP:
Gandollar
Duk da cewa ya samu kuri'u da dama lokacin da ya lashe zabe a karon farko a 2015, Ganduje ya fara bakin jini a idon wasu 'yan jihar jim kadan bayan hawansa mulki.
Hakan dai ba zai rasa nasaba da rikicin siyasar da ya barke tsakaninsa da mutumin da ya gada Sanata Kwankwaso tun kafin a je ko'ina, da kuma zargin cewa matarsa da aka fi sani da 'Goggo" tana tasiri matuka a harkokin mulkin jihar.