ATIKU: Abin da yasa nake kalubalantar nasarar da Buhari yayi
Dan takarar zaben shugaban kasa Atiku Abbakar wanda ya zo na biyu, ya bayyana dalilan sa na kalubalantar zaben da INEC ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi nasara.
Atiku ya rasa kujerar ta shugaban kasa ne, bayan da Buhari ya ba shi tazarar kuri’u sama da miliyan uku.
Tuni dai tun jiya INEC ta mika wa Shugaba Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo takardar shaidar cin zabe jiya Laraba.
Sai dai kuma Atiku ya ce ba zai taya Buhari murna ba, kuma ya kira zaben da cewa fashi da sata ce karara aka yi wa jama’a, na abin da ra’ayin su ya zabar musu.
A taron manema labarai da ya kira, Atiku ya buga misali da Akwa Ibom, ya ce tashinn farko akwai alamomin tambaya dangane da yadda aka samu raguwar wadanda suka yi zabe har zuwa kashi 62 bisa 100, duk kuwa da cewa wadanda suka yi rajista sun zarce wadanda suka yi a 2015.
Ya ce irin wannan tuggun aka kitsa a jihohi kamar Ribas, Delta, Abia da Benuwai.
Atiku ya yi mamakin yadda kashi 82 na wadanda suka yi rajista wai aka ce duk sun fito. Ya kara da cewa haka aka yi a yankuna da dama inda APC ta ke da magoya baya sosai.
Ya yi mamakin duk da matsalar tsaro a cikin jihar, amma a ce an jefa kashi 82 bisa 100 na adadin kuri’un wadanda suka yanki rajista.
Ya kara da cewa bai kuma yarda da sakamakon da ya nuna adadin kuri’un da PDP ta samu a Fadar Gwamnatin Tarayya, Kudu Maso Gabas da Kudu masu Kudu.
“Ba wai ina magana don na yi takarar shugaban kasa ba. Ni ina magana ne a matsayi nan a dan Najeriya, saboda duk wanda ya yi nazarin zaben nan da idon basira zai fahimci cewa babu yadda za a yi ace APC ta samu yawan wadannan kuri’u.
“A kan wasu dalilai da kuma wadannan da na bayyana ne na ke cewa ni Atiku Abubakar ban amince da sakamakon da INEC ta bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara ba.”
Ya yi kira ga magoya bayan sa su dau hakuri, domin ya na da yakinin cewa nasara a gare shi ta ke.
Premiumtimeshausa.