'Yan bindiga sun bude wa direbobi wuta a Zurmi

ZamfaraHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
'Yan bindiga sun bude wuta a kan direbobi a titin da ya ratsa karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara zuwa Gurbin-Baure.
Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar wani direba guda da kuma sace mutanan da ba a san adadin su ba.
Mazaunan yankin sun shaida wa BBC cewa da Misalin karfe uku da minti biyar na rana, 'yan bindigar suka tare hanya tare da bude wuta a kan masu wuce wa da kuma kona mota guda.
A cewarsu, kafin jami'an tsaro su isa yankin da abin ya faru 'yan bindigar sun tsere.
Wannan lamari ya haifar da fargaba tsakanin mazauna yankin da ke zaman dar-dar a yanzu.Sai dai a yanzu ana iya cewa an dan samu natsuwa sakamakon yadda jami'an tsaro ke kai komo.
An dai kashe daruruwan mutane a Zamfara a tsawon shekara shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.
Hare-haren da barayin shanu da masu satar mutane don kudin fansa ke yi a Zamfara na karuwa, duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen ayyukansu.
Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.
BBC
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post